Kyaftin din Ingila Harry Kane ya nuna kwarin gwiwar cewa za su “tsallaka” a karawar da za su yi da Denmark a ranar Laraba a zagayen semi-final, yana mai cewa kasar za ta kai wasan karshe a karon farko a gasar ta nahiyar turai.
Kungiyar kwallon kafa ta Brazil ta yi atisaye a ranar wasansu na kusa da karshe na Copa America da Peru a Rio de Janeiro.
Kwantiragin Lionel Messi a Barcelona ya kare a ranar 30 ga watan Yuni, abin da ke nufin dan wasan wanda dan asalin kasar Argentina ne na zaman kansa kenan.
Yanzu Ingila za ta hadu da Sweden ko Ukraine, wadanda za su kara nan ba da jimawa ba a birnin Glasgow.
Yanzu Switzerland za ta hadu da Spain wacce ta lallasa Croatia ita ma da ci 5-3.
Dan wasan Belgium Thorgan Hazard ne ya zira kwallon kafin a je hutun rabin lokaci, abin da ya kwaci kasar a karawar da suka yi a zagayen ‘yan 16.
Ronaldo: Portugal ta yi atisaye a filin wasa na La Cartuja da ke Seville ranar Asabar - sa’o’i 24 kafin su kara da Belgium a wasan zagaye na 16 na Euro 2020.
Sakamakon wannan wasa na nufin dukkan kasashen biyu, sun shiga zagayen ‘yan 16 da iyawar kowa za ta fisshe shi.
Cristiano Ronaldo yana atisaye da abokanan wasansa Raphael Guerreiro da Ruben Dias.
Magoya bayan Denmark suna murna a Copenhagen bayan sun zo na biyu a rukunin B na gasar cin kofin kasashen Turai 2020 da ya tabbatar da shigar su rukunin gasa na 16 yayinda suka lalasa Rasha da ci 4-1 a filin wasan Parken ranar Litinin.
Yanzu Pillars na matsayi na uku da maki 49 yayin da Akwa United ta dare sama da maki 53 a teburin gasar ta Premier a Najeriya.
Domin Kari