Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Belgium Ta Fitar Da Ronaldo A Gasar Euro 2020


'Yan wasan Portugal (Hoto: AP)
'Yan wasan Portugal (Hoto: AP)

Dan wasan Belgium Thorgan Hazard ne ya zira kwallon kafin a je hutun rabin lokaci, abin da ya kwaci kasar a karawar da suka yi a zagayen ‘yan 16.

Belgium ta yi waje-rod da Portugal a gasar cin kofin nahiyar turai ta Euro 2020 bayan da ta zira mata kwallo daya mai ban haushi.

Portugal ita ce take rike da kofin gasar.

Dan wasan Belgium Thorgan Hazard ne ya zira kwallon kafin a je hutun rabin lokaci, abin da ya kwace ta a karawar da suka yi a zagayen ‘yan 16.

Hakan na nufin Belgium za ta hadu da Italiya kenan a ranar Asabar.

Ita dai Portugal ta yi iya bakin kokarinta da aka dawo daga hutun rabin lokaci a kokarin da ta yi na farke kwallon, amma abin ya ci tura.

Belgium ta samu nasarar ce duk da cewa kyaftin dinta Kevin De Bruyne ya fita a wasan saboda raunin da ya samu bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci.

Ita ma kasar Czech Republic ta lashe wasanta bayan da ta doke Netherland da ci 2-0

A gobe za a kara tsakanin Spain da Croatia yayin da France za ta fafata da Switzerland

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG