Kungiyar wasan kare kai ta Karate ta Birni N'Konni, ta yi bikin gwajin nasarorin da ta samu a gasar karate ta kasa da ta wakana a garin Maradi, inda kungiyar ta zo ta 3 bayan Yamai da Maradi.
Dan wasan Jamhuriyar Tsakiyar Afirka Karl Namnganda ne ya zura kwallo a ragar Najeriya a minti na karshe a wasan wanda aka buga a ranar Alhamis a birnin Lagos da ke kudancin Najeriya.
Gabanin kalaman na Mbappe, Darektan wasannin kungiyar Leonardo ya fada cewa yana da kwarin gwiwar dan wasan zai sabunta kwantiraginsa da kungiyar.
Manchester United ta raba maki da Everton a wasan da suka buga bayan da aka tashi da ci 1-1 a gasar Premier League ta Ingila.
Tsohon dan wasan Najeriya Emmanuel Amunike ya yi kiran a samar da sauyi a fannin kwallon kafar kasa da kasa domin ba ‘yan wasan nahiyar Afirka damar kwarewa tare da kai wa ga buga wasa a fagen kwallon kafa na duniya.
Messi ya ci kwallon ce a minti na 74 bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci a wasan wanda ya City ta rika rutsa PSG.
Sai dai akwai wadanda suka yi hasashen cewa, Messi zai farfado kuma zai taka rawar gani a sabuwar kungiyar tasa ta PSG yayin da suke shirin karawa da Manchester City.
Rabon da Aston Villa ta doke Manchester United tun a watan Disambar shekarar 2009 a wasan da suka hadu a Old Trafford.
Har yanzu ba a ci Manchester United a gasar ta Premier ba cikin wasannin da ta buga, inda ta lashe hudu ta yi kunnen doki a daya.
Manchester United, wacce za ta kara da West Ham United a ranar Lahadi ta koma matsayi na biyu a teburin gasar.
Infantino na ziyarar kwana shida ne a Najeriya inda yake halartar gasar kwallon kafa ta mata da uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta shirya a tsakanin kasashe shida wacce ke gudana a Legas.
Liverpool ta lallasa AC Milan da ci 3-2 a wasansu na farko da suka buga a gasar cin kofin zakarun nahiyar turai na Champions League a wannan sabuwar kakar wasa
Domin Kari