Masoyan kungiyar Manchester United a sassan duniya na ta tafka muhawara a shafukan sada zumunta muamman a Twitter kan barar da fenariti da Bruno Fernandes ya yi a wasansu da Aston Villa.
Villa ta bi Manchester United har Old Trafford ta doke ta da ci 1-0.
Mai tsaron gidan Villa Kortney Hause ne ya zama zakaran wasan bayan da ya yi amfani da kansa ya zura kwallo a ragar David De Gea a minti na 88.
Rabon da Villa ta doke United tun a shekarar 2009.
Amma a minti na 90+5, United ta samu bugun fenariti bayan da Hause ya taba kwallon da hannunsa.
Sai dai Bruno wanda ya buga fenaritin ya zubar, inda ya doka kwallon ta tashi saman ragar Villa.
Hakan ya sa aka ta shi a wasan da ci 1-0.
Wannan nasara da Villa ta samu akan Manchester United bai yi wa masoyan United dadi ba lamarin da ya haifar da muhawara a shafukan sada zumunta.
Yayin da wa suke dora laifin akan Bruno da ya zubar da fenaritin wasu kuwa suna dora laifin ne akan rashin hadin kan ‘yan wasan na United.
“Sun nuna son kai a wasan, babu hadin kai, ya kamata a canja Ole, Man U na bukatar kocin da zai iya raya mashahuran ‘yan wasan.” In ji @Miky50326508.
“Greenwood da Bruno kwallon son kai suka buga, kowannensu yana so a ce shi ne zakaran wasan, sun manta cewa suna wasan ne a matsayin kungiya, abin kunya.” In ji @lamamamam.
“Ronaldo ya ji tsoron buga fenaritin, ba zai iya da nauyin da ya rataya a wuyansa na buga fenaritin a wannan lokaci ba.” @rentfreeiyh ya ce.
“Tsoro ba mahadin Ronaldo ba ne, abin da ka fada ba ma’ana.” @Mischief Ronnie ya mayarwa da @rentfreeiyh martani.
Mece ce makomar kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer?