Napoli ta yanke shawarar ci gaba da rike babban dan wasanta Victor Osimhen akalla na karin shekara guda kuma ba za ta saurari duk wani tayi daga kowace kungiya komin tsokar kudin da zasu taya a wannan bazara ba.
Yau ma mu na tafe da labarai masu armashi: Kama daga kan tsawaita kwangilar Diacre zuwa tsawaita kwangilar Jota zuwa fafatawar Venus da Rebecca da dai sauransu.
Ga dukkan alamu bangaren kwallon kafa a Najeriya zai samu bakuncin Yoshi Football Academy da ke Dubai a wani cigaba a fannin wasannin motsa jiki.
Yayin da damar karbar bakuncin garsar cin kofin Afurka ta 2025 ke neman kubucewa ma kasar Guinea, Najeriya ta ce a zo ga wuri.
Ga dukkan alamu, ana dada neman cinikin dan wasan Chelsea din nan dan asalin kasar Ghana, Abdul Baba Rahman, a yayin da ita kuma Chelsea ke cewa, idan ya na so, ana iya sayar da shi.
Wannan dai, shine karo na farko da Amina Seyni da ke rike da kambun tseren mita 200 na nahiyar Africa, ta halarci tseren na duniya.
Domin Kari