Dan wasan baya na dan asalin kasar Ghana, Abdul Baba Rahman, na tattaunawa da wani klub na premier league game da yuwuwar sayensa gabanin kakar wasa mai zuwa. Duk bangarorin biyu sun nuna sha'awa kuma bada jimawa ba za a kulla yarjejeniyar ta yanda Rahman zai koma wani sabon klub.
Rahman dai har yanzu dan wasan Chelsea ne, kuma yana karkashin yarjejeniya da klub din na premier har watan Yunin 2024. A daya bangaren, Chelsea ta nuna cewar dan wasan ba shi cikin shirye shiryenta kuma ta ma saka shi kasuwa. chelsea za ta tabatar da tarasfa zuwa wani klub muddun Rahman na so kuma yana ganin ya dace.
Yanzu haka kudin Rahman Euro milliyan 2.2 ne, wanda yafi Euro Milliyan 20 kasa da abinda Chelsea ta biya lokacin da ta saye shi daga Augsburg cikin 2015.
2023 CHAN Qualifiers: Black Galaxies To Depart Accra For Second Leg on Thursday
'Yan Black Galaxies Zasu Bar Ghana Zuwa Zango Na Biyu Gasar CHAN ta 2030 Ranar Alhamis
Alhamis 28 ga watan Yuli 'yan Black Galaxies na kasar Ghana za su bar birnin Accra don zagaye na biyu na wasan samun gurbi na zakarun kasashen Afurka da Junior Squirrels Benin. koci Annor Walker zai shiga wasan zagaye na biyu cikin kwanciyar hankali ganin ci uku da nema da su ka yi wa abokan karawarsu a ranar Lahadi a filin wasan Cape Coast.
Dan wasan gaba na Hearts Of oak Daniel Afriyie Barnieh ya bude raga wa Ghana acikin mintuna na 25 ,kan Mohammed Alhassan dake buga klub guda da shi; ya kara bayan mintin hudu. Bayan an dawo daga hutu kaftin din Ghana, Gladson Awako, ya karkare su, inda Ghana ta samu ci uku kasar Benin na nema.
'Yan Wasan Black Stars Da Ke Kasashen Waje Da Ke Hangen Gaba da Gasar Kofin Duniya Na 2022
Mai koyar da Black Stars Koci Otto Addo ya ce sabbin 'yan wasan Black Stars na hangen gaba da gasar cin kofin duniya na 2022 a Qatar, kenan wata dama ce ta iso a gare su. Kocin Ghanan ya ce 'yan wasan masu tinkaho da kasancewa 'yan kasa biyu na da burin 'yin abin fadi cikin gasanni da yawa da suka hada gasar cin kofin Afurka, karin halartar gasar cin kofin duniya da kuma fafatikan samun gurbi. Ana ta dai ikrarin 'yan wasan biyar da iyayensu 'yan Ghana suka haifa a Turai su yi anfani da damar gasar cin kofin duniya da za a yi a Qatar suka sahale makomarsu ga zakarun na Afurka a karo hudu.
CAF Na Shirin Dage Gasar AFCON Ta Neman Gurbi
Hukumar kwallon kafar Afurka (CAF) tana shirin dakatar da wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin Afurka ta 2023 zuwa watan Satumba. Tun farko a watan nan CAF ta bada sanarwar tunanin dakatar da gasar karshe ta cin kofin Afurka ta 2023 da aka shirya a cikin watan Janairu da Fabarairun 2024. Dan wasan CAF Dr Patrice Motsepe ya bada sanarwar dakatarwar gasar karshen, bayan wani taron kwamitin zartaswa da aka yi a Rabat kasar Morocco. Dr Motsepe ya bayyana cewar lalacewar yanayi a kasar ta Afurka ya yi tasiri wajen janyo tunanin sake tsara gasar cin kofin Afurka ta 2023 zuwa watan Janairun 2024.
Saurari rahoton Ridwan Abbas: