Masu sha'awar kwallon kafa da ma sauran jama'a a fadin duniya na ci gaba da nuna alhini kan rasuwar shahararren dan wasan kwallon kafan nan na kasar Brazil , Pele.
Shaharraren tsohon dan kwallon kafar kasar Brazil, Pele, ya rasu a yau bayan ya yi fama da jinya.
Arsenal ce dai take saman teburin gasar ta Premier da maki 37 inda Manchester City ke biye da ita da maki 32 sai Newcastle da maki 30.
A ranar 31 ga watan Disamba kwantiragin Michniewicz zai kare, kuma hukumar kwallon kafar kasar ta Poland ta ce ba za ta sabunta shi ba.
An watsa wasan ne cikin harsunan turancin Ingilishi da yaren sifaniya wadanda suka ba da wannan adadi.
Argentina ta doke Faransa da ci 4-2 a wasan karshe da bugun fenariti bayan da bangarorin biyu suka tashi da ci 3-3.
Kasar Argentina ta lashe gasar cin kofin duniya bayan ta doke Faransa mai rike da kofin a bugun fenareti da ci 4-2, bayan da suka tashi 3-3 bayan karin lokaci.
Wannan shi ne karo na uku da Argentina ke lashe kofin gasar, na farko a shekarar 1978 sai a 1986.
Kasar Croatia ce ta zo ta 3 a gasar kwallon kafar cin kofin duniya ta bana da ake fafatawa a Qatar, bayan da ta doke Morocco da ci 2-1 a wasan fitar da kasar da a zo ta 3 gasar.
Kocin Faransa, Didier Deschamps, ya ce yana da kwarin gwiwa dukkansu za su samu sauki kafin wasan karshe da za su buga da Argentina.
Wata mai baiwar zane-zane ‘yar kasar Paragua, wadda fitaccen dan wasan kwallon kafa na kasar Argentina Lionel Messi ya yaba baiwarta, tana baje kolin aikinta a Qatar inda ake gasar cin Kofin Duniya.
Domin Kari