Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dubban Mutane Sun Tarbi Tawagar Argentina A Buenos Aires


'Yan wasan Argentina akan motar bas zagaye da mutane a Buenos Aires
'Yan wasan Argentina akan motar bas zagaye da mutane a Buenos Aires

Argentina ta doke Faransa da ci 4-2 a wasan karshe da bugun fenariti bayan da bangarorin biyu suka tashi da ci 3-3.

Dubban mutane ne suka tarbi tawagar ‘yan wasan Argentina a Buenos Aires babban birnin kasar a ranar Talata a lokacin da ta sauka bayan lashe kofin duniya.

Argentina ta doke Faransa da ci 4-2 a wasan karshe da bugun fenariti bayan da bangarorin biyu suka tashi da ci 3-3.

'Yan wasan Argentina akan bas
'Yan wasan Argentina akan bas

Mutane sun yi cincirundo don su kyalla ido kan kofin gasar ta duniya wanda ‘yan wasan na Argentina suka zagaya da shi birnin, yayin da suke kan wata mota kirar bas mai budadden kai.

'Yan kasar Argentina a Buenos Aires
'Yan kasar Argentina a Buenos Aires

Wannan nasara da tawagar ‘yan wasan ta Argentina ta samu karkashin jagorancin Lionel Messi, na zuwa ne a daidai lokacin da matsin tattalin arziki ya addabi jama’a, nasarar da ake ganin ta zo a daidai lokacin da ake bukata, duba da cewa za ta sanyaya zukatan jama’a.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG