Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Croatia Ta Zo Ta Uku, Morocco Ta Bar Tarihi


Yan wasan kasar Croatia bayan samun nasarar zuwa na uku a gasar kwallon kafa ta duniya.
Yan wasan kasar Croatia bayan samun nasarar zuwa na uku a gasar kwallon kafa ta duniya.

Kasar Croatia ce ta zo ta 3 a gasar kwallon kafar cin kofin duniya ta bana da ake fafatawa a Qatar, bayan da ta doke Morocco da ci 2-1 a wasan fitar da kasar da a zo ta 3 gasar.

To sai dai za a iya cewa duk da wannan nasarar, Croatia din ta dan sami koma baya, domin kuwa ita ce ta zo ta 2 a gasar da ta gabata a shekarar 1998, lokacin da ta buga wasan karshe da kasar Faransa.

Lamarin da ke zama wata babbar nasara ga jagoran ‘yan wasan kungiyar Luka Modric, mai shekaru 37, wanda kawo yanzu ya bugawa kasar adadin wasanni 162, kuma ake hasashen wata kila wannan wasan ne na karshe da zai bugawa kasar Croatia.

A bangaren kasar Morocco kuma, duk da yake ta sha kashi ne a wasan, to amma kuma hakan bai shafi gagarumin sabon tarihin da ta kafa ba, na kasancewa kasar Afirka ta farko da ta sami kaiwa wannan matakin na gasar ta cin kofin duniya.

Yanzu haka kuma hankali ya karkata kan karon battar karfe da za a yi tsakanin Faransa da Argentina a wasan karshe ta gasar ta cin kofin duniya a ranar Lahadi.

Ra’ayoyi mabambanta kuma na ci gaba da karade wuraren tattaunawar jama’a, har ma da kafafen sada zumunta na yanar gizo, musamman dangane da babban gurin shahararren dan wasan kasar Argentina, na samun lashe gasar ta duniya, domin kafa babban tarihin da ba mai irinsa a duniyar kwallon kafa.

Da alama kuma wannan ce dama ta karshe ga Messi wanda ya lashe lambar gwarzon dan kwallon duniya har sau 7, ya kuma sami nasarori da dama, amma kuma bai sami daga kofin na duniya ba.

To sai dai a bangaren kasar Faransa, mai neman kafa tarihin zama kasa ta farko da ta sami lashe kofin na duniya sau 2 a jere a wannan zamanin, mai horar da ‘yan wasan kasar Didier Deschamps, ya ce ya na sane da dimbin jama’ar da ke fatan Argentina ta lashe gasar ta bana musamman saboda Messi, amma sam wannan bai dada shi da kasa ba.

Deschamps ya ce ya lura cewa an bar su su kadai a yayin da duniya ta karkata kan fatan nasara ga Messi da kasar sa ta Argentina, amma ya ce hakan ba zai shafi kuduri da kwazon sa da na ‘yan wasansa ba.

A nahiyar Afirka kuma kasar Afirka ta Kudu ta kaddamar da soma fafutukar neman damar karbar bakuncin gasar kwallon kafa ta cin kofin nahiyar Afirka ta shekarar 2025.

Hakan na zuwa ne bayan da aka tabbatar da kwace damar karbar bakuncin gasar daga kasar Guinea.

Idan kuma har kasar ta Afirka ta kudu ta sami damar, zai kasance karo na 3 kenan da take karbar bakuncin gasar ta nahiyar Afirka, bayan da ta karbi bakuncin gasannin na shekarat 1996 da 2013, wadanda kuma duk da farko an tsara gudanar da su ne a wasu kasashen na daban.

Kasar Kenya ce aka tsara za ta karbi bakuncin gasar ta shekarar 1996 amma kuma ta janye a kashin kanta, yayin da a shekarar 2013 kuma aka tsara gudanar da ita a kasar Libya, to amma yakin basasa da ya barke a kasar ya tilasta aka mayar da ita a kasar Afirka ta kudu.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG