Fushin magoya bayan Messi shi ne rahotanni da ke nuna cewa yana shirin barin PSG a karshen wannan kakar wasa, batun da har yanzu babu tabbaci.
Mutane da dama sun yaba da yadda Mbappe ya yi wa Neymar da Messi kara da ya fito ya kalubalanci hukumomin kungiyar ta PSG kan yadda ake yawan tallata shi.
A ranar Laraba kungiyar real Madrid ta je har gidan Barcelona ta jefa kwallaye guda hudu bayan da Barcelonan ba ta sami damar jefa kwallo ko guda ba.
Hakan na faruwa ne yayin da ake ta rade-radin dan wasan na Argentina na shirin barin kungiyar a karshen wannan kakar wasa.
Kungiyar ta Napoli ta sanar a karshen makon nan cewa Osimhen wanda dan asalin Najeriya ne, ya ji rauni a kafarsa ta hagu.
A halin da ake ciki hukumomin sun ce Pistorius na da wata dama a watan Agustan badi inda zai sake neman a sake shi da wuri.
Kungiyar Super Eagle ta Najeriya ta farfado inda ta rama ci 1-0 mai ban haushi da Guinea-Bissau ta yi mata a ranar Litinin.
A halin yanzu an nada mataimakinsa Cristian Stellini a matsayin mukaddashin mai horar da ‘yan wasan har zuwa lokacin kammala wannan kakar wasan.
Dan wasan gaba na kungiyar Bournemouth, Antoine Semenyo ne ya zura kwallo daya tilo a wasan inda Black Stars ta Ghana ta doke Palancas Negras ta kasar Angola a filin wasa na Baba Yara.
Wasu takardun kotu sun nuna cewa Barcelona ta biya dala miliyan 7.7 ga wani kamfani mai alaka da wani babban alkalin wasa.
Palacas Negras da ke shirya kece reni da ‘yan wasan Black Stars na Ghana a wassanin neman gurbin shiga gasar cin kofin Afrika, ta yi horon ne da karfe bakwai na dare.
‘Yan wasa 10 na kungiyar kwallon kafar Najeriya ta Super Eagles da ke taka leda a kasashen Turai sun isa Abuja babban birin kasar, gabanin fafata wasanni biyu na neman gurbin gasar cin kofin nahiyar Afirka da kasar za ta buga da Guinea Bissau.
Domin Kari