Tawagar ‘yan wasan Djurtus ta bai wa kowa mamaki a ranar Juma’a bayan da ta lallasa kungiyar Super Eagle da ci 1- 0 a Abuja.
Ko da yake, bugun fenarati da Moses Simon ya yi a zagayen farko na wasan, ya isa ya bai wa ‘yan wasan Jose Peseiro yi nasara a karawar.
Da wannan sakamakon, Najeriya ta koma ta daya a rukunin A da maki 9 inda ta bai wa ta biyu Guinea-Bissau maki biyu.
Wannan nasara da Super Eagles ta samu da ‘yar karamar tazara, ta kawo karshen rashin nasara a wasanni hudu da tawagar ta Najeriya ta yi a jere ba tare da ta lashe wasa ba.
Sau uku tawagar ta Najeriya tana lashe kofin gasar ta AFCON.
A halin yanzu, Saliyo ce ta uku da maki biyar a rukunin, yayin da Sao Tome & Principe take a karshen rukunin da maki daya kacal.