Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Messi Ya Haska A Wasansu Da Nice


Ligue 1 - OGC Nice v Paris St Germain
Ligue 1 - OGC Nice v Paris St Germain

Fushin magoya bayan Messi shi ne rahotanni da ke nuna cewa yana shirin barin PSG a karshen wannan kakar wasa, batun da har yanzu babu tabbaci.

Mako guda bayan da masoyansa suka yi masa ihun yankan kauna, Lionel Messi ya zura kwallo daya ya kuma taimaka an zura wata a karshen makon nan a karawar da suka yi da Nice.

PSG ta doke Nice da ci 2-0 tana kuma saman teburin gasar ta Ligue 1 da tazarar maki shida.

A minti na 26 Messi ya zura kwallon bayan da Nuno Mendes ya doka masa ita.

Nice ta yi ta samun dama iri-iri amma hakarta ba ta cimma ruwa ba.

Fushin magoya bayan Messi shi ne rahotanni da ke nuna cewa yana shirin barin PSG a karshen wannan kakar wasa, batun da har yanzu babu tabbaci.

A minti na 76 ne kuma Messi ya kwaso wata kwana daga hagu inda Sergio Ramos ya zura kwallo a ragar Nice.

Gabanin haduwarta da PSG, kungiyar ta Nice ta lashe wasanni 14 a jere ba tare da an doke ta ba a wannan kakar wasa.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG