Mai horar da ‘yan wasan kungiyar Tottenham a gasar Premier League ta Ingila Antonio Conte, ya ajiye aikinsa bisa ra’ayin kansa.
Kungiyar ta Tottenham ce ta sanar da tafiyar Conte wanda dan asalin kasar Italiya ne.
A halin yanzu an nada mataimakinsa Cristian Stellini a matsayin mukaddashin mai horar da ‘yan wasan har zuwa lokacin kammala wannan kakar wasan.
Sanarwar na zuwa ne mako biyu bayan wata sa-in-sa da aka yi inda Conte ya zargi ‘yan wasan kungiyar da son kansu da tare da sukar shugabannin kungiyar.
Conte ya kwashe watanni 16 yana horar da ‘yan wasan na Tottenham amma bai samu nasarar daga kofin na Premier ba wanda rabon da kungiyar ta ci tun a shekarar 2008.
Stellini ya taba jagorantar kungiyar ta Tottenham a lokacin da Conte yake jinyar wata tiyata da aka yi masa a kwanan nan.