Kasashen Najeriya, Morocco da Tanzania sun yi nasarar samun gurbin wakiltan Afrika a gasar cin kopin duniya na ‘yan mata kasa da shekaru 17 da za a yi a kasar India a cikin watan Oktoba.
A ranar Laraba Belgium za ta kara da Poland sannan ranar Asabar ta kara da Wales, amma dan wasan na Chelsea ba zai buga duka wasannin ba in ji Martinez.
Bale ya taimakawa Real Madrid ta lashe kofi 19, ciki har da na nahiyar turai guda biyar, inda ya zura kwallaye a shekarar 2014 da 2018 a gasar Champions League.
Magoya bayan Liverpool sun yi korafi kan tsaurara matakan da aka saka a kofar shiga filin wasan da kuma rashin tsari wajen shirya wasan, zargin da hukumomin Faransa suka musanta.
Ana gab da shiga wani sabon tarihi a duniyar kwallon kafa, yayin da aka kammala hada hadar sayar da shahararriyar kungiyar kwallon kafar Ingila din nan ta Chelsea, wadda sayar da ita ya biyo bayan takunkumin da aka kakaba ma mamallakinta mai barin gado, saboda alakarsa da Shugaba Vladimir Putin.
Wannan shi ne karo na 14 da Madrid take lashe kofin na Champions League.
Mane, wanda ya koma Liverpool a shekarar 2016, na da shekara daya kafin kwantiraginsa ya kare.
Kungiyar Milan ta ce an yi aikin kwaurin ne a Faransa, a kokarin da take yi don magance ciwon wanda ya jima yana addabar dan wasan.
A ranar Asabar Mbappe, ya shammaci mutane bayan da ya sanar da cewa zai ci gaba da zama a kungiyar ta PSG, lamarin da bai yi wa Madrid da magoya bayanta dadi ba.
Lahadin ake fafata wasannin karshe na gasar Premier ta bana, wadda rana ce da kungiyoyi da dama za su san matsayinsu, ciki har da wanda zai lashe gasar.
Klopp na nuna shakkun saka ‘yan wasan ne yayin da kungiyar ta Liverpool ke shirye-shiryen karawa da Real Madrid a wasan karshe na UEFA Champions League a ranar 28 ga watan Mayu da za a yi a birnin Paris na kasar Faransa
“Ina fatan ci gaba da zama anan har zuwa wasu karin shekaru masu zuwa sannan na kammala rayuwarta ta kwallo a nan.” Modric wanda dan asalin kasar Croatia ne ya ce.
Domin Kari
No media source currently available
1. Messi ne mafi cin kwallo a Argentina, kuma mafi taimakawa a ci kwallo 2. Babu wani a La Liga da ya taba cin kwallo da bugun ‘freekick’ fiye da Messi 3. A La Liga, Messi ne ya fi cin kwallo sau uku a wasa guda. 4. Babu shahararren dan wasan kwallon kafa da aka yi ta sa hotunansa a kwalayen...
Fitaccen dan wasan kwallon kafa Diego Maradona ya mutu bayan fama da matsalar bugun zuciya, a cewar mai magana da yawunsa.
Ga zabin VOA na jerin gwarzayen ‘yan wasan kwallon kafar Afirka biyar da za su buga wasa a yau. Wasu daga cikinsu sanannu ne – yayin da ta yi wu, ba ku san wasunsu ba…. tukuna. Su waye a jerin fitattun ‘yan wasanku a fagen kwallon kafar nahiyar Afirka a yau?