Hukumar da ke kula da gasar zakarun nahiyar turai ta UEFA, ta ce tana tattara hujjoji kan abin da ya faru a wajen filin wasa na Stade de France da ya karbi bakuncin wasan karshe na Champions League kamar yadda AP ya ruwaito.
A ranar Asabar, Real Madrid ta doke Liverpool a wasan karshen na gasar da ci 1-0.
Magoya bayan Liverpool sun zargi hukumar shirya wasanni a kasar ta Faransa da nuna rashin kwarewa yayin da ita ma gwamnatin Faransan ke zargin magoya bayan kungiyar ta Liverpool da haifar da turmutsitsi.
An dai samu turmutsitsi a wajen filin wasan da ke birnin Paris, lamarin da ya sa har aka jinkirta fara wasan da minti 30 duk da cewa a waje ne abin ya faru.
Magoya bayan Liverpool sun yi korafi kan tsaurara matakan da aka saka a kofar shiga filin wasan da kuma rashin tsari wajen shirya wasan, abin da ya kai ga ‘yan sanda suka yi ta fetsa hayaki mai sa kwallo, lamarin da ya rutsa da yara da masu manyan shekaru.
Wasu masu lura da al’amura sun ce gajeran lokaci da aka ba Paris na karbar bakuncin wasan a watan Fabrairu, na daya daga cikin abin da ya haifar da wannan turmutsitsi, bayan da aka karbe karbar bakuncin wasan daga hannun birnin St. Petersburg na kasar Rasha, saboda mamayar da ta yi wa Ukraine.