Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wacce Kungiya Sadio Mane Zai Koma Bayan Wasan Karshe Na Gasar UEFA?


Sadio Mane na Liverpool yayin wasan kwallon kafa na gasar Premier ta Ingila tsakanin Wolverhampton Wanderers da Liverpool a filin wasa na Molineux da ke Wolverhampton, Ingila, Asabar, 4 ga Disamba, 2021. (AP Photo/Rui Vieira)
Sadio Mane na Liverpool yayin wasan kwallon kafa na gasar Premier ta Ingila tsakanin Wolverhampton Wanderers da Liverpool a filin wasa na Molineux da ke Wolverhampton, Ingila, Asabar, 4 ga Disamba, 2021. (AP Photo/Rui Vieira)

Mane, wanda ya koma Liverpool a shekarar 2016, na da shekara daya kafin kwantiraginsa ya kare.

Ana ta samun rahotanni da ke nuni da cewa mai yiwuwa, wasan karshe na gasar zakarun turai da za a buga ranar Asabar a Paris tsakanin Real Madrid da Liverpool, shi ne zai zama wasa na karshe da Sadio Mane zai bugawa Liverpool.

Batun makomar dan wasan, wanda dan asalin kasar Senegal ne, ya zamanto babban al’amari a ranar Juma’ar nan yayin da manajan Liverpool Jurgen Klopp yake taron manema labarai a filin wasa na Stade de France a Paris.

Ko da yake, Klopp, ya gujewa saurin zartar da hukuncin cewa Mane zai ci gaba da zama a kungiyar ta Liverpool, yayin da rahotanni ke nuni da cewa zakarun Jamus, Bayern Munich na zawarcinsa.

“Yanzu ba lokaci ba ne da ya dace a yi magana kan wannan batu, duk kungiyar da Sadio zai bugawa a kaka mai zuwa, ba shakka, zai zamanto babban dan wasa.” In ji Klopp kamar yadda AP ya ruwaito.

Mane, wanda ya koma Liverpool a shekarar 2016, na da shekara daya kafin kwantiraginsa ya kare, kuma cikin ba’a ya ce sai an kammala wasan karshe na UEFA, zai ba da amsar ko zai zauna a Liverpool, ko zai kara gaba.

“Ku dawo ranar Asabar, zan ba ku amsar da kuke so ku ji.” Mane ya ce cikin raha.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG