A lokacin wasan, an soke kwallayen Haaland da Youssoufa Moukoko bayan da alkalin wasa ya ayyana cewa sun yi satar gida.
Dan wasan da ya fi haskawa a wasan shi ne, mai tsaron ragar Chelsea Kepa Arrizabalaga saboda kade fenariti biyu da ya yi.
Baya ta haihu a shirye-shiryen dan wasan kasar Argentina Lionel Messi, na komawa kungiyar PSG ta kasar Faransa, a yayin da lauyoyin Barcelona suka garzaya kotu, domin hana komawar ta shi.
Ana sa ran fitaccen dan wasan kwallon kafa Lionel Messi, ya isa birnin Paris na kasar Faransa a yau Litini don kammala shirye-shiryen komawa kungiyar PSG biyo bayan raba gari da Barcelona da ya bugawa wasanni a tsawon shekara 21.
“FC Barcelona na mika godiyarta ga dan wasan bisa irin rawar da ya taka wajen dabbaka kungiyar, tana kuma masa fatan alheri a duk in da zai je.”
Dan damben Ghana mai shekaru 20 Samuel Takyi ya kawo karshen shekaru 29 da Ghana ta yi ba tare da lambar yabo na damben boxing a Olympic bayan ya lallasa dan Colombia David Avila Ceiber a wasan matsayin featherweight a Olympic a Tokyo.
Dan wasan tseren Ghana mafi sauri, Benjamin Azamati-Kwaku ya roki ‘yan kasarsa gafara a kan gazawarsa na kai ga tseren maza na mita 100 a wasan karshe a wasannin Olympic shekarar 2020.
Tobiloba Amusan ‘yar Najeriya za ta yi wasan karshen na tseren mata na mita100 da ake tsallake shingaye a wasannin Olympic a birnin Tokyo na kasar Japan a ranarLitinin, bayan da ta samu gurbin shiga wasan karshen a yau Lahadi.
Domin Kari
No media source currently available
1. Messi ne mafi cin kwallo a Argentina, kuma mafi taimakawa a ci kwallo 2. Babu wani a La Liga da ya taba cin kwallo da bugun ‘freekick’ fiye da Messi 3. A La Liga, Messi ne ya fi cin kwallo sau uku a wasa guda. 4. Babu shahararren dan wasan kwallon kafa da aka yi ta sa hotunansa a kwalayen...
Fitaccen dan wasan kwallon kafa Diego Maradona ya mutu bayan fama da matsalar bugun zuciya, a cewar mai magana da yawunsa.
Ga zabin VOA na jerin gwarzayen ‘yan wasan kwallon kafar Afirka biyar da za su buga wasa a yau. Wasu daga cikinsu sanannu ne – yayin da ta yi wu, ba ku san wasunsu ba…. tukuna. Su waye a jerin fitattun ‘yan wasanku a fagen kwallon kafar nahiyar Afirka a yau?