Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Olympics: Dan Damben Ghana Mai Shekaru 20 Ya Lallasa Na Colombia Mai Shekaru 32


Samuel Takyi
Samuel Takyi

Dan damben Ghana mai shekaru 20 Samuel Takyi ya kawo karshen shekaru 29 da Ghana ta yi ba tare da lambar yabo na damben boxing a Olympic bayan ya lallasa dan Colombia David Avila Ceiber a wasan matsayin featherweight a Olympic a Tokyo.

A lokacin da dan Colombian mai shekaru 32 ya ke lallasan dan Ghanan kana ya samu maki da dama wurin alkalai yayin da suke shiga zagayen karshe na damben, Takyi ya farfado ya nuna kwarewa fiye da shekarunsa da kuma hazaka, ya kai wa zakaran Olympic sau biyu naushi bila’adadi ya yi nasarar sauya shan kaye da yake yi alkali uku suka ba shi maki kana biyu suka baiwa David maki, hakan ne kuma ya kai shi ga yin nasara da safiyar Lahadi.

Isarsa a wasan kusa da na karshe kawai, ta baiwa Takyi lambar yabo na akalla tgulla kafin ma ya fafata da ba-Amurken nan Duke Ragan a fadan kusa da na karshe, a ranar Talata 3 ga watan Agusta.

A boxing da ake yi a Olympic, duk wadanda basu yi nasara a wasannin kusa da na karshe ba, suna samun lambar yabo na tagulla, wanda hakan ke nufin Takyi zai samu lambar yabo ba tare da la’akari da sakamakon fadan ba.

Wannan ce lamabar yabo ta farko da Ghana zata samu a wasannin Olympic tun bayan da kungiyar kwallon kafa ta Ghana Black Meteors ta samu tagulla a Olympic a shekarar 1992 a Barcelona.

Wannan lambar yabon ita kuma ce ta hudu da Ghana zata samu a damben boxing a Olympic, inda Takyi ya karu da rukunin shaharrru da suka hada da Clement wanda ya samu azurfa a 1960 da Eddie Blay a shekarar 1964 da kuma Prince Amartey da dukkanin su suka samu tagulla, Takyi zai kuma zama namiji daya tilo daga Ghana da ya samu lambar yabo a wasannin Olympic.

Dan damben mai shekaru 20, y afara damben ne bisa kuskure inda ya sha lallasa a wurin kwararren dan damben Colombia, Avila Ceiber wanda ya samu maki wurin duk alkalai biyar.

A zagaye na biyu Samuel Takyi ya dan farfado a lokacin da ya yi amfani da tsawonsa yana tare abokin karawarsa mai shekaru 32, lamarin da a karshe ya kai shi ga samun amincewar alkalai uku cikin biyar.

Babban labari da ya fi dauke hankali shine dan Ghanan wannan ne farko da ya samu damar shiga wasannin Olympic.

Ya kwantar da hankalinsa yayin da kuma yake kai nushi mu nauyi a kan Ceiber Segura, wanda ke kara sukurkucewa da wasu dabaru marasa tasiri.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG