Chelsea, wacce ta lashe kofin zakarun nahiyar turai, ta sake lashe kofin UEFA Super Cup, bayan da ta doke Villareal da ci 6-5.
Kungiyar ta yi nasarar daga kofin ne bayan da aka tashi da ci 1-1 aka kuma kai ga bugun fenariti.
Dan wasan Chelsea Hakim Ziyech ne ya fara zura kwallo a ragar Villareal kafin daga baya ita ma ta farke kwallon, lamarin da ya kai ga karin lokaci da bugun fenariti.
Gerard Moreno ya zura kwallo a ragar Chelsea bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci.
Dan wasan da ya fi haskawa a wasan shi ne, mai tsaron ragar Chelsea Kepa Arrizabalaga da ya shigo a matsayin canji, saboda kade fenariti biyu da ya yi, abin da ya ba Chelsea ta Ingila damar doke Villareal ta kasar Sifaniya a wasan karshen.
Arrizabalaga ya maye gurbin Edouard Mendy ne a wasan, abin da ya ba shi damar nuna bajintarsa.
Nasarar Chelsea na zuwa ne bayan da ta doke Manchester City a watan Mayu a wasan karshe na gasar cin kofin zakarun nahiyar turai a karo na biyu.