Daruruwan 'yan gudun hijirar da tashe-tashen hankula ya raba da muhallansu a Jihar Taraba sun koka game da halin da suke ciki.
Matar Shugaban Najeriya Aisha Muhammadu Buhari da takwararta ta kasar China Ferfesa Peng Liyuan da wasu matan shugabanin kasashen Afrika sun halarci taron dakile cutar sida mai karya garkuwar jiki da aka gudanar a China.
A yau 4 ga watan Satumbar 2018, Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ne ya halarci taron zangon karshe na gasar kirkiro da fasaha ta dalibai a Jami'ar Bayero da ke Kano.
Kungiyar 'yan jaridu reshen jihar Sokoto, ta NUJ sunyi zanga zanga yau Alhamis
A jiya Laraba 29 ga watan Agustar 2018, Firai Ministan Burtaniya Theresa May ta kai ziyara a fadar shugaban kasar Najeriya.
Mataimakin shugaban kasa Prof Yemi Osinbajo ya hallarci Taron Lauyoyi Karo na 58 da ake yi a kowacce shekara
Gwamnan jihar Plato ya yi bukin Sallar layya a Daura tare da shugaba Muhammadu Buhari inda ya yi kira da a zauna lafiya domin ci gaban kasa.
Hukumomin Majalisar Dinkin Duniya masu kula da harkar cimaka da suka hada da WFP da FAO da IFAD sun amince zasu tallafawa jamhuriyar Nijar da Dala Biliyan 1.2 da kasar ke bukata, domin gudanar da aiyukan raya karkara a tsawon shekaru uku masu zuwa.
Domin Kari