Mutane Fiye Da Mutane 200 Suka Rasa Muhalinsu a Karamar Hukumar Maru ta Jihar Zamfara bayan tafka ruwan sama kamar da bakin kwarya.
Hotunan taron nakasassu na birnin Konni a lokaci ziyarar shugabaninsu na kasar Jamhuriyyar Nijar.
Toshon mataimakin shugaban kasa a Najeriya, Atiku Abubakar ya kaddamar da aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a inuwar jam’iyar adawa ta PDP.
Ministar tsaron kasar Faransa ta kai wata ziyara tare da takwaranta ta Nijar a sansanin sojin rundunar hadin guiwar G5 SAHEL dake garin OUALLAM na kan iyaka da kasar Mali.
Rundunar 'Yan Sandan Najeriya ta kama wasu mayaka da kwamandojin kungiyar Boko Haram, ciki har da wadanda suka tabbatar da cewa sun taimaka wajen sace 'yan matan Chibok daga makarantarsu.
Ministan Maikatan jiragen sama a Najeriya Sanata Hadi Sirika, ya kaddamar da fara aikin jirgin saman Nigerian Airways mai lamba 737 wanda ya dade da daina aiki tun shekarar 2003.
Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbanjo, tare da Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari a lokacin da ya kai ziyara Jihar Katsina, domin jajantawa kan ambaliyar da ta yi sanadiyar rayukan mutane a karamar hukumar Jibiya, inda kuma ya sa aka duba yanayin karfin ambaliyar da ta faru.
Mataimakin Shugaban kasar Najeriya, Yemi Osinbajo ya halarci taron masu saka hannun jari a bangaren kirkira da fasaha a masana'antar Hollywood a Amurka da ke birnin Los Angeles a Jihar California wanda manyan masu kamfanonin yin film suka halarta.
Domin Kari