Toshon mataimakin shugaban kasa a Najeriya, Atiku Abubakar ya kaddamar da aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a inuwar jam’iyar adawa ta PDP.
Ministar tsaron kasar Faransa ta kai wata ziyara tare da takwaranta ta Nijar a sansanin sojin rundunar hadin guiwar G5 SAHEL dake garin OUALLAM na kan iyaka da kasar Mali.
Rundunar 'Yan Sandan Najeriya ta kama wasu mayaka da kwamandojin kungiyar Boko Haram, ciki har da wadanda suka tabbatar da cewa sun taimaka wajen sace 'yan matan Chibok daga makarantarsu.
Ministan Maikatan jiragen sama a Najeriya Sanata Hadi Sirika, ya kaddamar da fara aikin jirgin saman Nigerian Airways mai lamba 737 wanda ya dade da daina aiki tun shekarar 2003.
Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbanjo, tare da Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari a lokacin da ya kai ziyara Jihar Katsina, domin jajantawa kan ambaliyar da ta yi sanadiyar rayukan mutane a karamar hukumar Jibiya, inda kuma ya sa aka duba yanayin karfin ambaliyar da ta faru.
Mataimakin Shugaban kasar Najeriya, Yemi Osinbajo ya halarci taron masu saka hannun jari a bangaren kirkira da fasaha a masana'antar Hollywood a Amurka da ke birnin Los Angeles a Jihar California wanda manyan masu kamfanonin yin film suka halarta.
Mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya kai ziyara a shalkwatar kamfanin google da ke California ta Amurka jiya 9 ga watan Yuli 2018, inda shugaban kamfanin Sundar Pichai ya tarbe shi.
Mutane na tsaye rike da rubutu kan kwali dake marhabun lalle wa matasa yan kwallo kafa da suka share sati biyu suna makale cikin kogon Tham Luang a kasar Thailand bayan masu ceto sun fitar da yara maza bakawai daga cikin 12 da suka makale a kogon July 9, 2018. REUTERS/Tyrone Siu - RC1369FF6F10
Domin Kari