Hukumar ta ICPC da kan yaki cin hanci a tsakanin jami'an gwamnati ta sha alwashin sakamakon taron ba zai zama zane kan ruwa ba.
A wata sanarwa da take fitarwa mako-mako, hukumar ta NCDC a rahotonta na mako na 35 ta ce an samu karin mutum biyar da cutar ta harba.
Rahotanni sun ce duk da an saki Ajaero, hukumar ta DSS ta kwace masa fasfo dinsa na tafiya.
Hukumomin al'ummomin da ke kan iyakar Najeriya da Nijar na kokarin dakile yaduwar cutar kwalara da ta bulla a birnin N'Konni na Jamhuriyar Nijar.
A cewar sanarwar, “an tsare Ajaero kuma har yanzu ba’a da tabbas game da inda yake ko kuma halin da lafiyarsa ke ciki, kasancewar duk wani yunkurin na tuntubarsa ya ci tura.”
Rahotanni sun bayyana cewar jami’an hukumar tsaron farin kaya ta DSS sun mamaye harabar ofishin SERAP dake Abuja, inda suka bukaci ganawa da daraktocin kungiyar.
Sai dai har yanzu ana cigaba da yin garkuwa da matarsa, Alkalin Majistare Binta Mshelia da direba da dogarinsa jami’in dan sanda.
Ministan Kudi da Tattalin Arzikin Najeriya, Wale Edun ya musanta rade-radin da ake yi na cewar an kara harajin cinikayya(vat) daga kaso 7.5 zuwa kaso 10 cikin 100.
A cewar Upah, kungiyar ba ta san inda aka tafi da Ajaero ba sai dai ya aiko da sakon wayar dake cewa hukumar tsaro ta DSS ce ta kama shi.
Cikin wata sanawar da ta fitar, hukumar ta NEMA ta ce cikin makonni masu zuwa jihohin Benue, Kogi, Anambra, Delta, Imo, Rivers da Bayelsa za su iya fuskantar mamakon ruwan sama da ka iya haddasa ambaliyar ruwa.
Kimanin Mutane hamsin da Dabbobi masu yawa ne suka kone kurmus a wani mummunan hadarin mota da ya auku a jihar Neja da yammacin ranar Lahadi.
Sabon shugaban hukumar alhazan Najeriya ta NAHCON Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan, ya yi alwashin yin tsayin daka a aikinsa bayan da aka bashi mukamin shuugabancin hukumar zan wajen sauke nauyin da a ka dora ma sa.
Domin Kari