Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Zan Ba Malamai Kunya Ba, A Cewar Sabon Shugaban Hukumar NAHCON


Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan
Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan

Sabon shugaban hukumar alhazan Najeriya ta NAHCON Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan, ya yi alwashin yin tsayin daka a aikinsa bayan da aka bashi mukamin shuugabancin hukumar zan wajen sauke nauyin da a ka dora ma sa.

A matsayinsa na babban malamin Islama da ya taba rike mukamin, Farfesa Pakistan ya ce ba zai ba malamta kunya ba wajen rikon amana.

A taron farko da ya gudanar da shugabannin sassa na hukumar, Farfesa Pakistan ya bukaci samun goyon baya daga dukkan ma’aikata, don ya na ganin aikin kamar dora jinka ne.

Shehun malamin ya ce tuni abokan huldarsa a Saudiyya daga hukumar alhazan kasar mai tsarki suka fara tuntubarsa don shirin aiki mai gamsarwa.

Hukumar Alhazan Najeriya
Hukumar Alhazan Najeriya

Ga shugaban hukumar da aka sauke bayan jagorantar aikin Hajjin bana, Malam Jalal Ahmad Arabi, Farfesa Pakistan ya ce sun yi masa addu’ar samun kwarin gwiwar rungumar kaddara.

“Ba mu ji dadin abin da ya same shi ba, don irin hakan ka iya samun kowa in ba a yi taka-tsan-tsan ba,” a cewar Farfesan.

Kwararre wajen lamuran aikin Hajji Ustaz Salisu Muhammad Gombe, ya ce ba taya murna kadai ya dace a yi wa sabon shugaban ba, akwai bukatar a yi masa addu’a.

Ustaz Salisu Gombe
Ustaz Salisu Gombe

Salisu Gombe ya ambaci hanyoyi biyu da ya ya ke ganin za a iya samun sauki a lamuran tsadar kujerar Hajji, na farko gwamnati ta shigo wajen tallafa wa ta bangaren farashin dala sannan ma’aikata su yi aiki ba tare da son zuciya ba.

Farfesa Pakistan ya yi karatu mai zurfi a Saudiyya da Pakistan inda ya ke wa’azi da jagorantar masallacin Jumma’a, musamman a Kano kafin ba shi wannan mukami.

Saurari cikakken rahoton:

Ba Zan Ba Malamai Kunya Ba, A Cewar Sabon Shugaban Hukumar NAHCON
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:48 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG