Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar DSS Ta Kama Shugaban Kungiyar Kwadago Joe Ajaero


A cewar Upah, kungiyar ba ta san inda aka tafi da Ajaero ba sai dai ya aiko da sakon wayar dake cewa hukumar tsaro ta DSS ce ta kama shi.

Hukumar tsaro ta DSS, ta kama shugaban kungiyar kwadagon Najeriya (NLC), Joe Ajaero.

An kama Ajaero ne a yau Litinin a tashar jiragen sama ta Nnamdi Azikwe dake Abuja a kan hanyar sa ta kai ziyarar aiki Burtaniya, a cewar kungiyar ta NLC.

Shugaban sashen yada labarai na kungiyar NLC, Mr. Benson Upah ne, ya tabbatarwa tashar talabijin ta Channels da batun kama Ajaero.

An tsara cewa Ajaero zai halarci wani taron kungiyoyin kwadago a birnin Landan, wanda za a fara a yau.

A cewar Upah, kungiyar ba ta san inda aka tafi da Ajaero ba saidai ya aiko da sakon wayar dake cewa hukumar tsaro ta DSS ce ta kama shi.

Kamen na sa na zuwa ne kimanin mako guda bayan da ya amsa gayyatar rundunar ‘yan sandan Najeriya akan abinda ta bayyana da bincike akan zargin daukar nauyin ta’addanci.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG