Lauyan hukumar EFCC, mai yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati a Najeriya, ne ya sanar da janye tuhume-tuhumen a gaban Mai Shari’a Emeka Nwite na babbar kotun tarayya dake abuja.
Hukumomin Najeriya na shirin sauya motoci miliyan 1 masu amfani da injinan man fetur zuwa amfani da iskar gas mai rahusa, ko CNG, nan da shekara ta 2027.
Netanyahu, kamar yadda rahotanni suka nuna a ganawar ta tsawon sa’o’i biyu da rabi, ya shaida wa Blinken cewa kisan Sinwar zai iya kawo “kyakkyawan tasiri” wajen sakin mutanen da aka yi garkuwa da su da kuma cimma burin Isra’ila na kawo karshen mulkin Hamas.
Wannan mummunan yanayi ya yi kama da wani lamari makamancin wannan da ya faru a Najeriya makon da ya gabata wanda ya yi sanadin mutuwar fiye da mutum 140, ciki har da yara kanana.
Akasarin asibitocin Najeriya za'a tarar akwai sassan kulawa da jarirai, da kananan yara da manyan mutane, sai dai yana da wuya a samu sashe mai zaman kansa inda ake kulawa da lafiyar 'yan mata matasa masu tasowa.
Majalisar ta ba da wa’adin makonni uku don kammala binciken a kuma gabatar mata da rahoto kan lamarin.
An sako shi daga gidan yarin kuje na Abuja ne bayan da ya shafe shekaru a gidan kaso, a yau Talata.
Ministan ya kuma baiwa mutanen da al"amarin ya shafa wa'adin zuwa ranar 27 ga watan Oktoban da muke ciki su kaurace daga gefen tituna.
Kamfanin samar da wutar lantarki na Najeriya (TCN) ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa wata matsala da ta samu a tashoshin samar da wutar lantarkin na Kainji/Jebba ne ya haddasa katsewar.
A yanzu haka dai CFA daya a kasuwar canjin kudi a Najeriya ta kai Naira 2800 nesa da dalar Amurka da ke wajajen Naira 1700.
A cewar Pullen batun fataucin miyagun kwayoyi wani babban al’amari ne na duniya baki daya, kuma kamar sauran manyan kalubale irinsu, sai duniya ta dauki manyan matakan yaki da shi.
Shugaban Karamar Hukumar Mariga, Abbas Musa Kasuwa-Garba, ya tabbatar da afkuwar harin tare da jajantawa iyalan wadanda al’amarin ya rutsa dasu.
Domin Kari