Wasu ‘yan kasuwar jamhuriyar Nijar a Najeriya na kokawa da yadda tsadar canja Naira zuwa CFA ke gurgunta harkokin kasuwancinsu.
A yanzu haka dai CFA daya a kasuwar canjin kudi a Najeriya ta kai Naira 2800 nesa da dalar Amurka da ke wajajen Naira 1700.
Kama daga kanana zuwa manyan ‘yan kasuwa na alaka da yanda Naira ke sauka ko tashi wajen canjin kudin ketare in an yi la’akari da tsadar da kan shafi dukkan kayayyaki hatta wadanda a ke samarwa a cikin gida.
‘Yan kasuwar na jamhuriyar Nijar da mu ka zanta da su a Abuja na cewa duk wani dalili da zai sa su dau Naira dake hannunsu don samun canjin kudin CFA na Faransa da su ke aiki da shi na zabtare musu jari don haka su kan nuksani wajen aika kasafin kula da iyali a gida.
Malam Umar Ahmad dan jamhuriyar Nijar ne dake kasuwanci a anguwar Garki a Abuja “gaskiya tun da canjin CFA ta baro ma na irun su N1000 ta zo ta kai N2000, yanzu ta na kusan N2800 gaskiya abin ya jijjigamu, mu da mu ke zuwa daga Nijar neman kudi a nan abun bai ma na dadi ba”
Shi kuma dan Nijar mai hada-hadar kudi ya ce dama ya hango faruwar hakan inda a ka bar Naira ta samu raguwar daraja ainun.
“Kun riga kun kada kudinku in ba kun bincika da kanku ba, ko an fahimtar daku ba zaku gane ba.
Yayin da gwamnan babban bankin Najeriya CBN Yemi Cardoso ke cewa bankin na kara daukar matakan dawo da darajar Naira masana tattalin arziki irin Yusha’u Aliyu na nanata cewa sai an yi gyara a cikin gida ta hanyar masana’antu, ciniki da Naira da rage almubazzaranci kafin ganin wani sauyi mai ma’ana.
Alkaluman hukumar kididdiga a Najeriya na nuna tashin farashin kaya ya haura kashi 32% da hakan ke dangantaka da faduwar darajar Naira.
Saurari rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya:
Dandalin Mu Tattauna