Hukumar kula da birnin tarayyar Najeriya, Abuja, ta gargadi mabaratan dake bara a gefen titi dasu bari ko kuma jami'an tsaro su kama su.
Ministan Abuja ne ya bayyana hakan a unguwar Katamfe yayin kaddamar da aikin hanyar data shiga sabon rukunin alkalai.
Ministan ya koka da cewar yawan mutanen dake rayuwa a gefen titi ya kai mizani mai tsoratarwa dake barazana ga tsaro a babban birnin.
Ministan ya kuma baiwa mutanen da al"amarin ya shafa wa'adin zuwa ranar 27 ga watan Oktoban da muke ciki su kaurace daga gefen tituna.
Ministan ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da rukunin gidajen alkalai 40 a birnin tarayyar.
Dandalin Mu Tattauna