A Najeriya, kimanin ‘yan mata miliyan 20 ne za su amfana da shirye-shiryen kula da lafiya tare da kyautata rayukansu a sauran fannonin rayuwa wanda kungiyar kyautata rayukan jama'a ta Plan International ke gudanarwa.
Yanzu haka kungiyar ta samar da wuraren kula da lafiyar 'yan mata matasa a asibitoci bakwai ta gyarawa gwamnatin jihar Sakkwato.
Akasarin asibitocin Najeriya za'a tarar akwai sassan kulawa da jarirai, da kananan yara da manyan mutane, sai dai yana da wuya a samu sashe mai zaman kansa inda ake kulawa da lafiyar 'yan mata matasa masu tasowa.
Wannan kuwa baya rasa nasaba da yadda wasu 'yan matan ke kyamar zuwa asibitoci saboda dalilai kamar kunya sannan ba kowa suke iya yi wa bayani matsalarsu ba.
Kungiyar Plan International Nigeria, ta bakin Daraktanta a Najeriya wanda ya maganta ta bakin Helen Idiom ya ce bincike da aka yi shekarar bara ya nuna kusan kashi 70 na 'yan mata matasa ba sa zuwa asibiti saboda ba su samun kebancewa su fadi bukatunsu cikin sirri.
A kan haka ne suka samar da sashen kula da 'yan mata a asibitoci bakwai da kungiyar ta gyarawa gwamnatin jihar Sakkwato.
Fatima Muhammad Rabo Jami'a mai kula da matasa a kungiyar ta Plan International ta ce wannan ba shakka zai yi tasiri wajen taimakawa 'yan mata masu bukatu na kula da lafiya idan suka je asibitocin.
Wannan ba shi kadai ne yunkurin kulawa da 'yan mata ba domin kungiyar ta tsara sai ayukkan ta yi kai ga mata kimanin milyan ashirin a Najeriya a cewar Helen Idiom.
Al'ummomi da suka amfana da wadannan ayukkan na gyaran asibitoci sun nuna gamsuwa da jin dadi akan wannan dauki da kasar Canada ta kawo musu ta hannun Plan International.
Kungiyar dai ta ce tana mayar da hankali ga kula da 'yan mata saboda bincike ya nuna kashi 78 cikin 100 na 'yan mata a arewacin Najeriya suna yin aure kafin shekaru 18 na rayuwa, kuma wasu na fara takalihin haihuwa tun suna shekaru 15, don haka akwai bukatar a mayar da hankali wajen ceton rayukansu ta fannoni mabambanta.
Saurari cikakken rahoton Muhammad Nasir daga Sakkwato:
Dandalin Mu Tattauna