Oyedepo yace ya na sa ran Yahaya Bello ya bayyana a kotu a ranar 14 ga watan Nuwamba mai kamawa, inda ya kafa hujja da wa’adin dake jikin sammacin na kwanaki 30, don haka ya bukaci a dage zaman kotun zuwa ranar 14 ga watan Nuwamba domin gurfanar da wadanda ake kara su 3.
Katsewar layin lantarki ya jefa yankunan arewa maso gabas da arewa maso yamma da wasu sassa na arewa maso tsakiyar Najeriya cikin duhu.
An ga wasu daga cikin mutanen dauke da bukitai, a yayin da wasu ke amfani da mazubai daban-daban wajen jidar man daga tankar.
Ya kara da cewa a jimullance, sau takwas tushen wutar na kasa yake rugujewa a shekarar 2024.
Hakan na faruwa ne yayin da aka tunkari zaben shugaban kasa, inda dan takarar jam’iyyar Republican, Donald Trump, ya mayar da batun shige da fice a matsayin babban batu.
Harin ya zo ne bayan sa’o’i kadan da ake zargin 'yan tawaye Kurdawa sun ta da bama-bamai da kuma bude wuta a kamfanin sararin samaniya da tsaro na TUSAS.
Sai dai kotun ta ba Munju zabin biyan Naira miliyan 100 kan tuhume-tuhume guda biyu da aka mata kan laifukan da ta aikata.
A zazzafar mahawarar da fiye da sanatoci 20 suka tafka, an bayyana matsalar yaran da basa zuwa makaranta da wani bam dake daf da fashewa, dake bukatar daukar matakan da suka zarta na gwamnatin tarayya kawai.
Tuhume-tuhumen sun hada da zargin cin hanci da rashawa da wawure kudade da karkatar da dukiyar al’ummar da ta kai bilyoyin nairori.
A yau Laraba, an bada rahoton cewar ‘yan sanda na kokarin tarwatsa wani gungun karuwai ‘yan Najeriya a garin Limassol na Cyprus sakamakon kama wasu mata 3 da aka yi, da hadin gwiwar hukumar yaki da safarar mutane na kasar.
Asusun, a hasashensa na bunkasar arzikin duniya na baya-bayan nan (WEO), yace hasashen bunkasar arzikin Najeriya na 2024 da ya wallafa a rahotonsa na baya ya ragu daga kaso 3.3 zuwa 2.9 cikin 100.
Shugaban kasar ya sallami ministar harkokin mata, Uju-Ken Ohanenye da ta yawon bude ido; Lola Ade-John da ministan ilimi, Tahir Mamman da karamin ministan gidaje da raya birane, Abdullahi Gwarzo da kuma Jamila Ibrahim, ministar ci gaban matasa.
Domin Kari