Asusun bada lamuni na duniya (IMF) ya zaftare hasashen da yayi akan bunkasar arzikin Najeriya saboda raguwar yawan danyen man da take haka da tsananin ambaliyar ruwa da sauran kalubalen dake tarnaki ga cigaban tattalin arzikinta.
Asusun, a hasashensa na bunkasar arzikin duniya na baya-bayan nan (WEO), yace hasashen bunkasar arzikin Najeriya na 2024 da ya wallafa a rahotonsa na baya ya ragu daga kaso 3.3 zuwa 2.9 cikin 100.
Ya dora alhakin raguwar a kan, tasirin hauhawar farashin kayayyaki na baya-bayan nan da ambaliyar ruwa da kuma raguwar yawan danyen man da ake haka.
Sai dai hasashen da asusun ya yi a kan bunkasar arzikin duniya a 2025 yana a kan kaso 3.2 cikin 100 bai sauya ba.
Hasashen bunkasar arzikin duniyar ya nuna raguwar kaso 0.1 cikin 100 daga wanda ya yi tunda fari a watan yulin 2024.
Ga Najeriya, hasashen bunkasar arzikin da asusun IMF ya yi na 2025 ya nuna karuwar kaso 0.2 cikin 100 daga wanda ya yi tunda fari a watan Yulin bara.
Bunkasar arzikin a 2024 zai tsaya a kan kaso 2.9 cikin 100-inda aka samu koma baya idan aka kwatanta da hasashen da aka yi a watan Yulin daya gabata, a cewar IMF
Game da hauhawar farashi, an yi hasashen cewar matsalar za ta tsaya a kan kaso 25 cikin 100 a 2025 da kaso 14 cikin a 2029.
Dandalin Mu Tattauna