A cewar wata majiya a masarautar ta Kano, jami’an tsaro dauke da manyan makamai, ciki har da motocin sulke, sun yiwa kofar shiga fadar kawanya, tare da takaita zirga-zirga.
Hedkwatar Rundunar sojojin saman Najeriya ta ce ta kwato bindigogi sama da dubu takwas da dari biyu, da kuma sama da harsasai dubu dari biyu daga hannun 'yan ta'adda a baki daya sassa daban daban na kasar.
Kasar Amurka ta jaddada aniyar ci gaba da bayar da tallafi a Najeriya da kuma inganta shirin yadda zai kara kyautata rayukan 'yan kasar.
‘Yan majalisar sun hada da Esosa Iyawe (daga jihar Edo) da Tochukwu Okere (daga Imo) da Donatus Mathew (daga Kaduna) da Bassey Akiba (daga Cross River) da Kuma Daulyop (daga Filato).
A watan Disamban 2023, Majalisar Dattawa ta bayyana shirin gudanar da cikakken bincike a kan hukumar dake kula da fanshon sojoji.
Direba da ma’aikatan jirgin sun yi nasarar juya akalarsa zuwa filin jirgin saman Maiduguri tare da yin saukar gaggawa domin kaucewa bala’i.
Majalisar wakilai ta dauki wani mataki da wasu ke gani abin alheri ne bayan jin irin koke koken da suka rika tashi kan batun korar ma'aikata 1,000 da Babban Bankin Najeriya ya ce zai yi, yayinda kwararru a fanin tattalin arziki ke gani akwai bukatar kyakkyawan karatun ta natsu kan lamarin.
An sake samun tashin wata nakiya da ake zaton 'yan bindiga ne suka dasa ta a jihar Zamfara da wata Motar fasinja ta bi kai, ta kashe mutun biyu daga cikin matafiyan tare da jikkata wasu da dama daga cikin su.
Barau, wanda ya jagorancin zaman majalisar, yace kudurorin sun janyo cece kuce, inda yace an dorawa kwamitin alhakin tuntubar Antoni Janar na Tarayya, da bangaren zartarwa da sauran muhimman masu ruwa da tsaki.
A cewarsa, hatsarin ya afku ne da kimanin karfe 10 na dare a kauyen Chelluri mai tazarar kilomita 20, a kan hanyar Bayamari zuwa Geidam dake jihar.
A yau Laraba, ‘yan bindiga suka dasa jerin sabbin nakiyoyi a yankin Mai Lamba na babbar hanyar Dansadau zuwa Gusau dake karkashin karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara, inda suka hallaka matafiya.
Har yanzu tana kasa tana dabo kan wanda ya gina jerin gidajen da kotu ta mallakawa Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa a birnin Tarayya Abuja.
Domin Kari
No media source currently available