Yawan kasashen dake fama da cutar Polio dai ya ragu daga kasashe 125 a shekarar 1988 zuwa kasashe 3 rak a yanzu: watau Najeira, Pakistan da Afghanistan.
Wani sabon rahoton da aka buga kan rayuwar kananan yara ya nuna cewa Nigeriya bata sami wani ci gaba ba a daukar maatakan maganin mace macen kananan yara a cikin shekaru goma da suka wuce.
Za a gudanar da aikin bayar da rigakafin na Polio ga yara a kasar ta Syria da wasu sassan Iraqi, Jordan, Lebanon da Turkiyya.
Kashi 13% na kananan yaran da suke mutuwa kafin su cika shekaru biyar suna faruwa ne a Nigeriya domin rashin tsabta.
Rabon da a ga jinsi na 3 na kwayar cutar Polio tun watan Nuwambae 2012 a Najeriya, da kuma watan Afrilun 2012 a kasar Pakistan
Kwararu sun bayyana cewa, za a iya amfani da wata irin kwayar rigakafin HIV dake tsayar da kwayar cutar kanjamau daga shiga cikin wurin kariyar jiki, wajen aiki kan cutar kansa nan gaba, yayinda kamfanonin magani suka hada magunguna wuri daya.
Ministan lafiya, Farfesa Onyebuchi Chukwu ya bada umurni ga ma’aikatar kiwon lafiya ta kasa ta shiga aiki a jihohin da aka sami barkewar cutar kwalera kwanannan, da ta kashe kimanin mutane 80 a jihohi 7.
Gwamnatin tarayya ta baiyyana damuwar ta bisa ga karuwar yawan mutuwa daga barkewar cutar kwalera a kauyen Namu cikin karamar hukumar Qua’pan a jihar Plato.
Fiye da mutane 80 ake tsammani sun mutu ta wurin cutar kwalara tun barkewar cutar a shiyoyi daban daban na Najeriya.
Wani baban masanin kiwon lafiya, Dr. Ahmed Gana, yayi bayanai masu muhimmanci a kan cutar sankarau.
Hukumar Kiwon lafiya ta Duniya ta tabbatar da kamuwar yara 10 a lardin Deir al-Zour na yankin arewa maso gabashin Syria.
Hukumar lafiya ta duniya tace gubar dalma tana da hatsarin gaske musamman ga kananan yara.
Domin Kari