Amma duk da haka, akwai kyakkyawan labari a wannan yaki da ake yi da cutar ta Polio.
A ranar lahadi aka cika shekara daya daidai da ganin karshe da aka yi ma jinsi na Uku na kwayar cutar Polio, wani abinda ke karfafa guiwar cewa watakila gwagwarmayar bayarda rigakafin cutar Polio da ake yi ta samu nasarar kawar daya daga cikin jinsuna biyu na kwayar cutar Polio da suka rage a duniya.
Idan har da gaske ne jinsi na 3 na kwayar cutar Polio ya bace, wannan yana nufin cewa yanzu saura jinsi na 1 na kwayar cutar kawai ya rage a duniya.
Cika shekara guda cur da aka yi ba tare da an ga jinsi na 3 na kwayar cutar ba, yana ba wadanda ke da hannu a wannan yaki mai tsada kuma mai cin rai, kwarin guiwar cewa watakila an samu nasarar kawo karshen yaduwarsa a duniya.
Amma masanan suka ce har yanzu ba su shirya gudanar da bukin murnar kawar da jinsi na 3 na kwayar cutar ta Polio ba tukuna.
Masanin kwayar cutar Polio a Cibiyar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Amurka, CDC, Olen Kew, yace "bayanin da muke da shi a hannu mai karfafa guiwa ne. amma ga batun Najeriya musamman, ina jin cewa zamu nemi karin shaida kafin mu ce zamu yi murnar kawo karshen yaduwar jinsi na 3 na cutar."
An samu jinsi na 3 na kwayar cutar Polio na karshe a Najeriya cikin watan Nuwambar 2012. A Pakistan, daya daga cikin kasashen da har yanzu suke fama da cutar, ta ba da rahoton ganin jinsi na 3 na kwayar cutar Polio na karshe tun watan Afrilun 2012. Dakin binciken Cibiyar CDC ta Amurka dake sanya idanu kan yaduwar kwayoyin halittar cuta a duniya, ya bada rahoton cewa a cikin shekaru biyun da suka shige, an yi ta samun raguwar kwayoyin cutar Polio masu alaka da jinsi na 3 a duniya.
Cibiyar CDC tana daga cikin cibiyoyin da suka hadu suka kirkiro da Shirin Kawar da Cutar Polio daga doron duniya a shekarar 1988. Sauran wadanda aka kafa wannan yunkuri da su sune Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya, WHO, da Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF da kuma kulob din Rotary International. A cikin 'yan shekarun nan, Gidauniyar Bill da Melinda Gates ta shiga cikin wannan kokarin gadan-gadan.