Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za A Yi Ma Yara Miliyan 20 Rigakafin Polio A Gabas Ta Tsakiya


Rigakafin cutar Polio a kasar Syria
Rigakafin cutar Polio a kasar Syria

Za a gudanar da aikin bayar da rigakafin na Polio ga yara a kasar ta Syria da wasu sassan Iraqi, Jordan, Lebanon da Turkiyya.

Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya da kuma Asusun tallafawa Yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, sun ce ma'aikatan kiwon lafiya zasu yi kokarin ba yara miliyan 20 maganin rigakafin cutar shan inna ko Polio a yankin Gabas ta Tsakiya, a wani yunkurin dakile mummunar barkewar cutar da aka gani a can.

Yankin na Gabas ta Tsakiya, ya shafe shekaru 10 ba tare da samun bullar cutar Polio ko sau daya ba, kafin a gano wani jinsin kwayar cutar da ya samo asali daga Pakistan cikin ruwan kwatami na Misra a watan Janairu.Tuni aka samu irin wannan jinsin kwayar cutar aruwan kwatami a Isra'ila da Gaza da Yankin Yammacin kogin Jordan. A watan da ya shige, an tabbatar da cewa wasu yara su 10 da kafafuwansu suka shanye, sun kamu da cutar ta Polio ce.

Za a gudanar da aikin bayar da rigakafin na Polio ga yara a kasar ta Syria da wasu sassan Iraqi, Jordan, Lebanon da Turkiyya.

Sake bullar cutar Polio a yankin gabas ta tsakiya zata iya yin barazana ga kasashen Turai a saboda akwai 'yan kasar Syria dake neman mafaka a can, yayin da akwai 'yan yawon shakatawa da bude ido dake ziyartar Isra'ila.

Amma kuma babban jami'in yaki da cutar Polio na hukumar WHO, da kuma babban likitan hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, sun yi watsi da wannan hasashen, su na masu fadin cewa ai akwai kasashe irinsu Najeriya da Somaliya da Pakistan inda ake fama da wannan cuta sosai, kuma su na da al'ummomin kasashensu masu yawan gaske a Turai da Amurka, amma ba a taba jin sun kai cutar can ba.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG