Ms. Greening ta fadawa taron Kungiyar Ritary International na duniya a Milton Keynes dake Buckinghamshire, cewa sake bullar cutar ta Polio a Syria da kuma yankin gabashin Afirka na yin barazanar mayarda hannun agogo baya a ci gaban da aka samu wajen kawar da wannan cuta daga doron kasa.
Ministar ta bayarda sanarwar sakin Fam miliyan 100 domin taimakawa yunkurin ganin bayar wannan cuta ta Polio. Wannan wani bangare ne na kudi Fam miliyan 300 da Britaniya ta yi alkawarin bayarwa domin samar da rigakafin polio ga yara miliyan 360 nan da shekarar 2018.
Wannan sanarwa nata tana zuwa a daidai lokacin da adadin masu kamuwa da wannan cuta a duniya ya karu. Yawan kasashen dake fama da cutar Polio dai ya ragu daga kasashe 125 a shekarar 1988 zuwa kasashe 3 rak a yanzu: watau Najeira, Pakistan da Afghanistan.
A bara, yawan yaran da suka kamu da Polio guda 223 aka samu a duk fadin duniya. Amma a bana, Somaliya ta samu bullar Polio a karon farko tun 2007. Haka kuma an bayarda rahoton bullar cutar a makwabtan Somaliya irinsu Kenya, da Ethiopia. A watan da ya shige, an tabbatar da bullar cutar Polio a karon farko cikin shekaru 14 a kasar Syria.
Justine Greening ta ce, "A shekarar 1988, an samu rahoton bullar cutar Polio har sau dubu 350. A bara, yara 223 kawai aka samu. A saboda kokarin da duniya take yi na takalar wannan cuta, ciki har da muhimmin aikin da kungiyar Rotary International take yi, yanzu mun yi kusan cimma gurinmu na mayar da cutar Polio ta zamo sai a littattafan tarihi kawai zaa rika karanta ta."