Dr. Tijani Husseini, mukadashin direktan kiwon lafiyar jama'a da takaita yaduwar cututuka a ma'aikatar lafiya a jihar, yayi bayani cewa sun fara ganin karuwar masu amai da gudawa makonni hudu da suka wuce. Ya kuma ce, a ka'ida idan aka sami wannan yanayi, duk wanda aka tabatar yana da cutar, sai a bi shi zuwa gida domin tsabtace mahalinshi.