Hukumar abinci da magunguna ta kasar Ghana tana gargadin jama’a, musamman asibitoci, wuraren shanmagani, wurin saida magani da sauran wuraren kiwon lafiya, game da kasancewar wani maganin zazzabin cizon sauro mara kyau a kasuwannin kasar Ghana, mai suna – kwayoyin Quinine Sulphate (300mg).