Ministan lafiyar Najeriya Dr.Halliru Alhasan ne ya fadi haka a wata tattaunawa da Sashen Hausa na Muryar Amurka
Yayinda 'yan kungiyar Boko Haram ke cin karensu ba babbaka suna haddasa kashe-kashe, kone gidajen mutane tare da raba mutane da muhallansu a jihohin Adamawa, Borno da Yobe kungiyar nakasassun jihar Bauchi ta dukufa akan addu'o'in neman zaman lafiya.
Hukumomi a Saliyo sun umurci mutane su dakata a gidajensu na tsawon kwanaki uku a wannan watan.
Dangane da rade-radin da ake yi cewa cutar Ebola, ta bulla a jihar Kaduna, batun baida alamar kanshin gaskiya, ko kadan.
Ana daukan matakan da suka kamata wajen ganin cewa cutar ebola da ta kunno kai a Fatakwal bata bazu ba. Idan ba'a yi hakan ba lamarin ka iya jawo mummunar illa ga rayuwar jama'a da ma tattalin arziki.
Yayin da Najeriya ke samun yabo daga kasashen duniya akan hobbasan da tayi na ganin ta dakile yaduwar cutar ebola sai gashi a karon farko wani likita ya rasu amma ba a Legas ba inda cutar ta fara, a jihar Rivers sanadiyar cutar ta ebola.
Duk da gina asibitoci da gwamnati keyi da wuya a samu isassun magunguna da kayan aiki musamman a yankin karkara.
Ministan ilimin Najeriya Malam Ibrahim Shakarau ya karanta bayanin tsawaita hutun makarantun firamare da sakandare da makonni shida a duk fadin kasar domin a haras da malamai akan yadda zasu binciki yaran makarantunsu su gano masu dauke da kwayar cutar ebola.
Ganin yadda jihar Borno ke makwaftaka da kasashen Afirka uku yasa uwargidan gwamnan Borno ya sa Hajiya Nana Kashim Shettima ta shirya taron fadakar da kawunan jama'a akan cutar ebola
Majalisar zartaswa karkashin shugabancin shugaban kasa Jonathan ta karbi rahoton kwamitin yaki da cutar shan inna.
Sabanin maganganun da a keyi na cewa cutar ebola cuta ce da idan an kamu da ita ba makawa sai mutuwa amma batun ba haka yake ba domin mutane biyar cikin wadanda suka kamu da cutar sun mike kuma likitoci sun tabbatar basu dauke da kwayar cutar a jikinsu yanzu.
Domin Kari