Dangane da rade-radin da ake yi cewa cutar Ebola, ta bulla a jihar Kaduna, batun baida alamar kanshin gaskiya, ko kadan.
Ko da yake batun ya cike yanar gizo [wato internet] inda masu yada jita-jita ke cin karansu babu babbaka wajen yada wannan labarin na karya, kamar yanda aka yada batun sha da wankarn gishiri.
Wakilin muryar Amurka, Nasiru Yakubu, Birnin Yero, yace hukumomin jihar kaduna, sun tauki matakan wayarwa da jama’a kai a game da wannan cutar, domin tabbatar da kariya ga jama’a.
Ya kara da cewa duk da wannan kokarin da gwamnatin jihar Kaduna ta keyi, karyar kanzon kurege na neman shafe kokarin da take yi.