Hukumomin a Najeriya na bayyana damuwa kan karuwa da ake ci gaba da samu a adadin masu kamuwa da cutar korona birus a kasar inda cibiyar kula da cututtuka masu saurin yaduwa ta NCDC ta bayyana cewa an samu karin mutane dubu 1 da 56 da suka kamu da cutar a ranar talata kadai.
Sakamakon wani bincike da Jami’ar Oxford ta fitar yau Laraba ya nuna cewa maganin rigakafin korona birus da kamfanonin AstraZeneca da Jami’ar ta Oxford suka samar, yana rage yaduwar kwayar cutar da kashi biyu bisa uku.
Ma'aikatar lafiya ta Najeriya tace gwamnatin kasar na bukatar kudi kimanin nera biliyan 400 don kaddamar da allurar rigakafin cutar korona.
Tattaunawa da Dr. Muhammed Gazzali Hashim na Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano game da ciwon kunne a wajen jariri da ke iya haddasa rasa ji idan ba'a dau matakin magance matsalar ba,
Yayin da ake cigaba da bayyana farin cikin samun maganin corona mai ingancin kashi 90 cikin 100, kwararru sun ce a bi a hankali, kai a yi watsi da batun sanya takunkumin baki. Hangen Dala, ba shiga birni ba.
Gwajin rigakafin cutar coronavirus da kamfanin Pfizer ya samar, ya nuna sakamako mai kyau da ya wuce yadda aka yi tunanin samu a baya.
Tattaunawa da Babban Darektar Hukumar dake yaki da Cuta Mai Karya Garkuwar Jiki wato HIV/AIDS (NACA) a Najeriya, Dr. Gambo Aliyu game da ayyukan hukumar. Kashi na 2.
A yau 3 ga watan Nuwamba, masu kada kuri’a a New Jersey, zasu yanke hukunci kan ko a halatta amfani da tabar Wiwi a hukumance.
Alkaluma Jami’ar Johns Hopkins dake kididdigar masu dauke da cutar coronavirus na nuni da cewa Amurka ta zarra da adadin wadanda suka kamu da coronavirus mutum miliyan 9 a juma’ar nan, inda aka samu sababbin kamuwa miliyan 1 a cikin makonni biyu.
A jiya Litinin hukumar kiwon lafiya ta duniya ta WHO ta sake yiwa kasashe kashedi cewa a daina saka siyasa a harkar annobar COVID-19, tana mai cewa yin haka na kawo rudani da rashin girmama masana kimiya kana cutar na kara ta’azzara.
Domin Kari
No media source currently available
Wani kamfnin wasan bidiyo ya kaddamar da wani wasa da nufin karfafawa maza masu jinni a jika guiwa, su motsa jiki a wannan yanayin da ake fama da annoba da nufin taimakawa a rage gallazawa mata.
An yi kiyasin cewa, kimanin kashi 8% na al’ummar duniya ba su cin nama kwata-kwata. Masu kula da lamura sun ce, irin wannan rayuwar na iya zama da kalubale a kasashen nafiyar Afirka inda ake yawan cin nama da kuma kifi a galibin abincin da aka saba da shi.
Madina Shettima Pindar, kwararrar mai kula da abinda ya shafi cin abinci mai gina jiki a asibitin kwararru na birnin Maiduguri, jihar Borno a Najeriya, ta yi karin haske kan tasirin cin abinci ba nama.
Har yanzu ana cikin duhu dangane da sabon nau’in annobar COVID 19 Omicron, da ya hada da tasirin rigakafin COVID-19 da kuma, ko akwai bukatar samar da wani maganin rigakafi.