Bayan shafe shekaru masu yawa a yaki da cutar shan inna, hukumar lafiya ta duniya ta ayyana Afrika a matsayin nahiyar da ta barranta daga cutar shan inna bayan Najeriya ta samu shekaru 4 ba tare da bullar cutar ba.
Tun lokacin da duniya ta shiga cikin mawuyacin hali bayan barkewar annobar cutar Coronavirus, ko COVID-19, rayuwar gaba daya ta canza, kuma babu tabbacin ko zata koma daidai.
A jiya litinin Fadar White House ta sanar da cewa mai bawa shugaban Amurka shawara kan harkokin tsaro Robert O’Brien ya kamu da COVID-19.
Wurare da yawa da suka samu nasarar farko a yaki da coronavirus, yanzu suna ganin sabbin kamuwa da cutar bayan da suka sassauta dokokin kulle, cikin su har da Vietnam, Australia da kuma Hong Kong.
Hukumar dakile yaduwar cututtuka a Najeriya, (NCDC), ta fitar da alkalumma a kan yakin da take yi da yaduwar COVID-19 a wani sakon Twitter a jiya Litinin.
Hukumomi a Amurka na duba yiwuwar amincewa da wani shirin ba al'umar kasar wasu karin kudaden tallafi domin rage radadin da cutar coronavirus ta haifar a kasar.
Domin Kari
No media source currently available
Wani kamfnin wasan bidiyo ya kaddamar da wani wasa da nufin karfafawa maza masu jinni a jika guiwa, su motsa jiki a wannan yanayin da ake fama da annoba da nufin taimakawa a rage gallazawa mata.
An yi kiyasin cewa, kimanin kashi 8% na al’ummar duniya ba su cin nama kwata-kwata. Masu kula da lamura sun ce, irin wannan rayuwar na iya zama da kalubale a kasashen nafiyar Afirka inda ake yawan cin nama da kuma kifi a galibin abincin da aka saba da shi.
Madina Shettima Pindar, kwararrar mai kula da abinda ya shafi cin abinci mai gina jiki a asibitin kwararru na birnin Maiduguri, jihar Borno a Najeriya, ta yi karin haske kan tasirin cin abinci ba nama.
Har yanzu ana cikin duhu dangane da sabon nau’in annobar COVID 19 Omicron, da ya hada da tasirin rigakafin COVID-19 da kuma, ko akwai bukatar samar da wani maganin rigakafi.