Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

COVID-19 Ta Sake Kunno Kai A Kasashen Da Suka Yi Nasara A Baya


Coronavirusta sake tashi a wasu kasashe
Coronavirusta sake tashi a wasu kasashe

Wurare da yawa da suka samu nasarar farko a yaki da coronavirus, yanzu suna ganin sabbin kamuwa da cutar bayan da suka sassauta dokokin kulle, cikin su har da Vietnam, Australia da kuma Hong Kong.

Vietnam ta sanr jiya Litinin za ta kwashe masu yawo bude ido daga yankin Danang bayan da aka tabbatar da mutane da dama suka kamu da kwayar cutar da ke hadasa cutar COVID-19.

A ciki wata sanarwa gwamnatin Vietnam ta ce aikin kwashe mutane 80,000, wanda yawancin su masu yawon bude idon cikin gida ne, zai dauki akalla kwana hudu. Kasar kuma za ta cigaba da kasancewa a kulle ga baki ‘yan kasashen waje masu yawo bude ido.

Vietnam a ranar Asabar ta fada cewa bazuwar cutar a cikin kasar tun daga watan Afrilu, yasa gwamnatin cikin shirin ko ta kwana. Kasar dai ana mata kallon wacce ta yi nasara wajan yaki da barkewar cutar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG