Yayin da alkaluma ke nuna cewa adadin wadanda ke kamuwa da cutar COVID-19 na ci gaba da karuwa a Amurka, a yau Litinin ake sa ran ‘yan Jam'iyyar Republican a Majalisar Dattawan kasar za su gabatar da wani kudurin ba da tallafi.
Ana tunanin cewa tallaffin zai kai kudade dala tiriliyan daya domin sassauta radadin da annobar coronavirus ta haifar a kasar.
Shirin na zuwa ne kwanaki gabanin karewar wa’adin ba da agajin kudade na farko ga miliyoyin Amurkawa da suka rasa ayyukansu sanadiyyar cutar ta COVID-19.
A jiya Lahadi, bayan da aka kwashe kwanaki ana tattaunawa da ‘yan Republican a majalisar dokokin kasar, shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Amurka, Mark Meadows da kuma Sakataren Baitul- Mali Steven Mnuchin sun ce tallafin ya kunshi fadada shirin ba da kudaden ne ga wadanda suka rasa ayyukansu.
Amma a cewarsu, a wannan karo, Amurkawa za su ga kashi 70 cikin 100 ne na kudaden da aka ba su a baya.
A dai ranar Juma’a wa’adin tallafin farko zai kare wanda aka biya wasu kunshin kudade ga wadanda suka rasa ayyukansu, aka kuma rika ba su 600 a kowanne mako baya ga wanda jihohi suke bayarwa.
Su dai ‘yan Republican suna korafin cewa wannan shiri na nufin wasu mutanen da ake biya na samun kudaden da suka haura wanda ake biyansu a lokacin da suke aiki, idan aka hada tallafin gwamnatin tarayya da wanda jiha ke biyansu.
Amma ‘yan Democrat a nasu bangaren, sun kalubalanci wannan ikrari suna masu cewa lura da yadda cutar ta coronavirus ke karuwa, wasu ma’aikatan ba su da kwanciyar hankalin da za su iya komawa bakin aikinsu.
Facebook Forum