Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sami Bullar Ciwon Shan Inna A Ethiopia


Dan yaro yana karban maganin cutar shan inna
Dan yaro yana karban maganin cutar shan inna

Kasar Ethiopia ta bada ruhoton samun bullar cutar shan inna guda biyu (WPV-1), wanda ya kawo yawan wadanda aka samu da kwayar cutar a kasar zuwa uku wanda, adadin kuma yana karuwa a yankin na Africa

Kasar Ethiopia ta bada ruhoton samun bullar cutar shan inna guda biyu (WPV-1), wanda ya kawo yawan wadanda aka samu da kwayar cutar a kasar zuwa uku wanda, adadin kuma yana karuwa a yankin na Africa.

Ruhoton cibiyar yaki da cutar shan inna (GPEI) ya bayyana cewa sake samun bullar cutar a Ethipoi ya sa yawan dawanda suke dauke da cutar a yankin ya kai 191, wanda ya hada da sababbi biyar da aka samu a Somalia.

Kananan yaran da aka samu dauke da kwayar cutar shan innnan dukansu suna bangaren yankin Somalia wurin da aka sami bullar kwayar cutar a baya.

Sashen Somali na Ethopia yana ci gaba da yin gagarumin aikin rigakafi tun watan Yuni lokacin da aka maida bangaren a matsayin wanda yake cike da hadarin yada cutar.
Rohoton hukumar yaki da cutar shan inna-GPEI ya nuna cewa kasar ta kara maida hankali wajen yaki da cutar, ta wajen ilimantar da jama’a ta radiyo da telebijin da kuma rikakafi da kari a kan iyakar Ethopia da Somalia da kuma sauran hanyoyin yada labarai domin kawar da wannan cutar.

Ana ci gaba da ayyukan rigakafi a yankin da suka hada da Ethiopia da Somalia da Kenya, da kewayen sashin Yemen. Ba a sami wani sabon rahoton bullar cutar ba a kasashe uku da ake fama da cutar watau, Pakistan, Afghanistan da Nigeria.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG