Kasar Ghana ta yi bikin cika shekaru 30 da mulkin dimokradiyya a jamhuriya ta hudu, da kundin tsarin mulkin 1992 da ya samar. a shekarar 2019, gwamnatin shugaba Akufo-Addo, ta kebe duk ranar 7 ga watan Janairu, a matsayin ranar tunawa da dimokradiyar Ghana.