Kundin tsarin mulkin kasar Ghana na shekarar 1992, shi ne wanda ya fi dadewa tun bayan da Ghana ta samu 'yancin kai a shekarar 1957, bayan juyin mulkin 1960 da 1970 da kuma 1981. Tun shekarar 1992, ba a samu rahoton yunkurin juyin mulki a Ghana ba.
Dan jarida, Salihu Shuaibu Sarauta ya ce, bayan matsin lambar da ya sa tsohon shugaban kasa, marigayi Jerry John Rawlings, ya dawo da mulki zuwa na dimokradiya ne ya sa aka hada wannan kundin tsarin mulkin.
Gwamnati ta kafa kwamitin nazarin yi wa kundin tsarin mulkin kwaskwarima a shekarar 2010, amma, har yanzu da kwamitin ya kammala aikinsa, kuma ya mika rahoton, ba a aiwatar ba. Shi ya sa masana da kungiyoyin matsin lamba suka sake farfado da kiraye-kirayen sake bitar kundin.
Yunus Swalahudeen Wakpenjo ya ce kundin tsarin mulkin ya baiwa bangaren zartarwa, musamman shugaban kasa karfi fiye da Majalisar dokoki, wanda hakan ya sa ake samun matsalolin tattalin arziki da tsaro a kasar.
Yayin da ake bukin ranar kundin tsarin mulkin a fadin kasar, daruruwan al'ummar kasar suna yin zanga-zangar lumana a birnin Tamale dake Arewacin Ghana, a karkashin jagorancin kungiyar matsin lambar nan ta #fixthecountry, domin a sauya wannan kundin tsarin mulkin. Jerin gwanon ya bi ta manyan titunan Tamale a karshe, jagoran kungiyar Oliver Barker Vormawor ya yi jawabi.
"Mun damu da jama'a da kuma tsarin mulkin da ke tuhumar shugabannin siyasa ba tare da la'akari da jam'iyya ba. Idan ku matasa ne na jam'iyya, gobe ina rokon ku da ku jagoranci tawaga zuwa ofisoshin jam'iyyar ku, ku ba da sanarwar neman sabon kundin tsarin mulki ga mutanen Tamale. Su fitar da tsarin mulki wanda zai inganta rayuwar al’umma. Wannan shi ne alhakin siyasa".
Lauya me zaman kansa, Dokta Hamisu Mohammed, ya bayyanawa Muryar Amurka cewa, ba domin jimawar kundin tsarin mulki yake sa a sauya shi ba, duk da cewa akwai wasu sashe-sashe dake bukatar a yi musu kwaskwarima a wannan kundin na 1992, musamman sashen da ya ba da damar nada minista daga majalisar dokoki. Ya ce, haka zai sa su kasa gudanar aikinsu yadda ya kamata
A rana ta 7 ga watan janairu ake rantsar da sabon shugaban kasa da 'yan majalisar dokoki, bayan an gudanar da babban zabe na kasa.
Domin karin bayani saurari rahotan Idris Abdullah: