‘Yan sandan Uganda suna gudanar da bincike a kan wani turmutsitsi da ya faru ranar jajijibirin sabuwar shekara a birnin Kampala, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 9, ciki har da yara da dama.
Hukumar tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a Ghana da ake kira National Peace Council ta bukaci gwamnati ta dauki matakin ladabtar da wasu gidajen rediyo a yankin Bawku da ke gabashin Ghana.
A kammala gasar kokowar gargajiya karo na 43 a jihar Diffa da ke jamhuriyar Nijer ranar Asabar.
Ibtila'in fashewa a garin Appiate da rikicin kabilanci a garin Bawku, yarjejeniya da asusun lamuni na duniya (IMF), ce-ce-ku-cen tsige Ministan Kudi, hauhawar farashin kayayyaki da tsadar rayuwa. zanga-zangar kungiyoyin kwadago da na farar hula.
Majiyoyin soji da na cikin gida sun sanar a jiya Juma’a cewa wani harin kwantan bauna da mayakan jihadi suka kai a yankin arewa mai nisa na kasar Kamaru ya hallaka wani soja.
Masu sha’awar kwallon kafa a Jamhauriyar Nijar kamar sauran takwarorinsu na sassan duniya sun bayyana alhini a game da rasuwar fitaccen dan kwallon Brazil Pele.
Ana dada samun karin bayani kan musabbabin rasuwar shahararren dan wasan kwallon kafan nan na kasar Brazil, Pele
A cigaba da takaddamar da ake yi kan batun sauya fasalin naira, Majalisar Dattawan Najeriya ta bukaci Babban Bankin Najeriya (CBN) da ya tsawaita wa'adin canja kudade a Najeriya.
Masu sha'awar kwallon kafa da ma sauran jama'a a fadin duniya na ci gaba da nuna alhini kan rasuwar shahararren dan wasan kwallon kafan nan na kasar Brazil , Pele.
Shaharraren tsohon dan kwallon kafar kasar Brazil, Pele, ya rasu a yau bayan ya yi fama da jinya.