Shugaban kasar Nijer ya fara rangadi a jamhuriyar Benin, don tantauna da takwaransa kan batutuwa da dama da suka shafi huldar kasashen biyu, a daidai lokacin da ayyukan ta’addanci daga arewacin Mali ke shafar kasashen biyu.
Masana harkokin tsaro sun bayyana gamsuwa da abin da suka bayyana a matsayin kusancin da aka fara samu a tsakanin hukumomin Nijar da na Mali, wadanda a baya ba sa ga maciji sakamakon juyin mulkin da soja suka yi a kasar ta Mali.
Hukumar kula da samar da abinci ta MDD ta tallafa wa ‘yan gudun hijirar cikin gida a jihar Tilabery ta Jamhuriyar Nijar da kudade da nufin sassauta wahalwalun da suka shiga na tserewa daga matsugunansu na asali sanadiyar aika-aikar ‘yan ta’addan arewacin Mali.
Yayin da ake bukin ranar Alkalai Mata ta Duniya, kasar Ghana ta doshi cika muradun ci gaba mai dorewa (SDG) na Majalisar Dinkin Duniya tare sa samun kashi 50 cikin 100 na yawan mata alkalai a shekarar 2030, wanda zai baiwa mata damar ba da gudunmarsu wajen tabbatar da adalci.
Kimanin mayakan Bokon Haram 40 ne suka mika wuya ga hukumomin jihar Diffa a Jamhuriyyar Nijar a wani mataki na karba kiran hukumomin jihar na ganin mayakan na boko haram sun mika wuya domin samun kulawa ta musamman a wata cibiyar gyara halinka dake garin.
Takwas ga watan Maris din kowace shekara, rana ce da ake bikin mata ta duniya inda taken bana ya mai da hankali kan bukatar samar da daidaito a tsakanin jinsi.
A ranar Mata ta duniya dubban mata sun fita kan tituna a kasar Kamaru don nuna adawa da tsadar rayuwa. Sai dai gwamnati ta dora alhakin hauhawar farashin kayan abinci da makamashi kan mamayar da Rasha take a Ukraine.
A yayinda a yau Laraba 8 ga watan Maris ake bukukuwan ranar mata ta duniya mata a kauyen Kouraye dake jihar Zinder a jamhuriyar Nijer sun dukufa ka’in da na’in a karkashin wani shirin da hukumar WFP da FAO da asusun IFAD suka kaddamar.
Shugaban gundumar birnin N'Konni, Malam Ralisu Aili, ya yabawa jami'an tsaron a game da wannan namijin kokarin da suka yi kana ya ce wannan zai taimaka wajen kare al'ummar.
An gudanar da bikin wannan shekarar a birnin Ho dake yankin Volta. Shugaban kasar Guinea Bissau, kuma shugaban kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afirka ta yamma (ECOWAS), Umaro Sissoco Embalo, ne babban bako na musamman a bikin bana.
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron da ke rangadi a wasu kasashen yankin tsakiyar Afrika ya yi ikirarin cewa zamanin siyasar uwar daki da ‘yan korenta a tsakanin Faransa da kasashen Afrika ya wuce.
Shugaba Akufo-Addo ya yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki a zaben shugaban kasar Najeriya da aka kammala, da su yi sulhu cikin lumana ga dukkan wata takaddama da ta taso.
Domin Kari