NIAMEY, NIGER - Daruruwan mutane maza da mata ne suka hallara a dandalin garin Ballayara na jihar Tilabery domin karbar tallafin da hukumar PAM ta saba bayar wa a kowane wata ga magidantan da tashin hankalin da ake fusknta akan iyakar Nijar da Mali ya tilastawa arcewa.
Kamar yadda aka saba a wannan karon ma kowa ya zo dauke da tikitinsa a hannu.
Wata mata Hassiatou Ousseini dattijuwa da ta karbi na ta rabon ta bayyana mana farin ciki a game da wannan yunkuri.
Ta ce tashin hankali ne ya koro mu amma tun da muka zo nan ba mu fuskanci kowace matsala ba, muna yi wa PAM godiya da tallafin da take ba mu.
Ta kara da cewa ni tsofuwa ce, ba zan iya aikin karfi ba amma duk da haka ina kira ga PAM da ta taimaka mana da kayan aiki koma wane iri ne domin ba zai yiwu mutum ya jira kullum sai dai a ba shi ba.
Boureima Issaka magidancin dake dauke da nauyin mutane a kalla 14 ya kwatanta tasirin wannan tallafi a gare su ‘yan gudun hijirar cikin gida.
Lalacewar al’amuran tsaro a jihar Tilabery sakamakon yadda ‘yan ta’adda ke cin karensu ba babbaka a kasashen Mali da Burkina Faso ya sa al’umomin garuruwan dake kan iyakar Nijar tserewa daga garuruwansu don zuwa neman mafaka a wuraren da ba mahalli ba kuma aikin yi ko wata madogara, dalili kenan da WFP ke tallafa masu da dan abin masarufi.
Abdoulaye Sarre shugaban karamin ofishin PAM mai kula da jihohin Tilabery da Dosso, ya ce ayyukan rabon tallafi ga ‘yan gudun hijirar cikin gidan Tilabery abu ne da ke gudana a dukkan manyan biranen gundumomin jihar, saboda nan ne mafakar irin wadanan mutane da suka tsere daga garuruwansu ba shiri. PAM ce ke ba su tallafin abinci a kowane wata.
Ya ce "nan muna Ballayara inda akasarin mutane suka gudo daga Banibangou saboda hare-haren da aka yi fama da su, akalla sun kai mutane 4000 a nan inda PAM ke taimaka masu da abinci."
Matsalolin tsaro a jmhuriyar Nijar wani al’amari ne da ya samo tushe daga aika-aikar ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda a kasashe makwafta wato Najeriya, Mali da Burkina Faso.
An kuma yi katari lamarin na zuwa a wani lokacin da illolin canjin yanayi ke kara tsananta, wanda kai tsaye ke shafar sha’anin noma da kiwo a kasar da kashi 80 a cikin 100 na al’ummar da ke zaune a karkara.
Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma: